Labarai
A gaggauce: Ganduje ya haramta sayar da sinadaran ƙarin armashin lemo a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta haramta sayar da sinadaran haɗa lemo da ake zargin sun haifar da cuta a jihar.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban hukumar kare haƙƙin masu saye da masu sayarwa ta jihar Baffa Babba Ɗanagundi.
A cewar sa, sinadaran da aka haramta cinikiyyar su a jihar Kano na ta ke, sun haɗa da sinadaran haɗa lemo irin su Foster Clark da Critic Acid da kuma Jolly Juice da sauran sinadaran ƙarin armashi da ake haɗa lemo ko Awara ko kuma kunun tsamiya da su.
Baffa Babba ya kuma ce, Gwamnati ta umarci hukumar sa da ta fara kama masu sayar da irin waɗannan kayayyaki.
A don haka ya roƙi jama’a da su fallasa dukkan wanda suka samu yana sayar da irin waɗannan sinadarai.
Karin labarai:
An karɓi sakamakon farko game da sabuwar cutar da ta ɓulla a Kano
Kano: Mutane 167 ne suka kamu cutar fitsarin jini a mako guda
Baffan ya ce, tuni aka baza jami’ai a sassan Kano domin sanya idanu tare da kame masu wannan sana’a.
Wannan dai ya biyo bayan ɓarkewar wata annoba da ta kama sama da mutane 160 a jihar.
Ana dai zargin annobar na da alaƙa da kayyakin da aka sarrafa da sinadaran.
Sai dai tuni ma’aikatar lafiya ta Kano ta yi gwaji ga masu ɗauke da cutar aka kuma aika babban ɗakin gwaje-gwaje na ƙasa da ke Abuja domin bincike.
To amma a nasu ɓangaren ƙungiyar masu sayar da irin waɗannan sinadarai ta jihar Kano, ta ce wasu ɓata-gari ne suka haifar da matsalar.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Abubakar Isah Muhammad ya shaida wa Freedom Radio cewa, tuni suka ɗauki gaɓarar yaƙi da ɓata-garin.
You must be logged in to post a comment Login