Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Nishadi

A gidajen kallo kawai muke son sakin fim din Radhe na Salman Khan – Prabhu Deva

Published

on

Gwani wajen koya rawa kuma mai bada umarni Prabhudeva ya ce, har idan akwai wanda zai dawo da Jindadin ‘yan kallo a gidajen kallo a kasar India to kuwa bai wuce fitaccen jarumi Salman khan ba.

Prabhu Deva na bayyana hakan lokacin da yak e jawabi kan sakin sabon fim din nan mai suna “Radhe”.

Ya cewa babu yadda za’ayi a saki sabon fim din Salman khan a yanar Gizo kamar yadda Al’ada take a yanzu, har ma ya ce da ba’a bude gidajen kallo ba to za su yi ta Jira har lokacin da za’a bude.

Daraktan fim din na Radhe wato Prabhudeva ya kuma ce “lokacin da muka fi bukata Shine lokutan hutu wanda za mufi dawo da ‘yan kallo kamar Lokutan bikin Diwali da na Kirsimeti na wannan Shekara ta 2020 ko kuma Republic day na 2021 yana mai cewa har kawo yanzu dai bamu yanke hukunci ba”

Tun a ranar sallah babba ta wannan Shekarar aka yi kokarin sakin sabon fim din sai dai kuma barkewar annobar Corona ta janyo aka dakatar da sakin fim din mai suna “Radhe” na Salman khan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!