Addini
Abin takaici ne lauyoyi musulmai ke bada kariya ga Yahaya Sharif -Gidauniyar Empathy
Gidauniyar Empathy mai tausayawa da tallafawa al’umma da ke nan Kano, ta nuna takaicin ta bisa yadda wasu lauyoyi musulmi da kuma wasu daga kudancin kasar nan ke kokarin bada kariya ga Yahaya Shrif Aminu.
Yahaya Aminu wanda kotu ta yankewa hukuncin kisa a nan Kano, sakamakon furta kalaman batanci ga fiyayyan halitta Annabi Muhammad S.A.W.
Shugaban gidauniyar Mansur Musa Gabari ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da tashar Freedom Radio game da yadda aka samu lauyoyi da kokarin yiwa dokar Allah Kwaskwarima.
Ya kuma ce, duk mutumin da ya amsa sunan sa musulmi ya kuma sanya hannu don kare mutumin da ya yi batanci ga Annabi ya yi Ridda.
Mansur Musa Gabari, ya kara da cewa kamata ya yi duk wani lauya daya kasance musulmi ya bada tasa gudunmowar don ganin an zartar da hukuncin da kotu ta yanke ga wanda yai batanci ga annabi Muhammad S.AW.
A cewarsa, duk wani musulmi kamata ya yi ya fifita ma’aiki Annabi Muhammad SAW akan duniyarsa da iyalinsa da ma kansa, don samun dacewa.
You must be logged in to post a comment Login