Manyan Labarai
Abinda yasa EFCC zata binciki Kwankwaso da wasu mutane
Hukumar ya ki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, zata binciki tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bisa kan zargin karkatar da kudin makamai sama da biliyan 35.
Daga cikin wanda hukumar ta EFCC, zata bincika har da tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya na zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ,Chief Mike Oghiadomhe, sai Adetekunbo Kayode, da dukkanin su tare da tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso wanda yana rike d amukamain ministan tsaro a wancan lokaci kan karkatar da sama da biliyan 35, na kudaden siyan makamai da kwantiragin siyo su.
Jaridar Thisday ta rawaito cewa , cikin wadanda hukumar zata bincika har da tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar tsaro Dakta Haruna Sunusi, da Manjo Janar Nguni.
Bincike ya tabbatar da cewa, kwantiragin siyo makaman anyi shi ne don samar da makamai da sauran kayan aiyyukan gudanar da tsaro ga tawagar sojin kasar nan dake aiyyukan samar da tsaro a kasashen duniya.
Siyasa: Shin ritayar da Ganduje yayiwa Kwankwaso ta tabbata?
Kwankwaso mutum ne mai son kansa-Ganduje
Shin rigimar Ganduje da Kwankwaso tazo karshe?
An dai ranto kudaden daga ofishin lura da basussuka na kasa wato debt Management office (DMO) don siyan makaman ga rundunar Sojin.
Kakakin hukumar ta EFCC, Mista Tony Orilade, ya tabbatar da gudanar da binciken inda yace wasu daga cikin kwantiragin ba a kammala su ba, ya yin da wasu kuma kawai an yi shaci fadin biyan su wanda a zahiri ba ayi ba.
Hukumar ta EFCC, ta ce zata cigaba da bincike don tabbatar da yadda aka karkatar da kudaden karkashin wani babban kamfanin kwangila, da yanzu haka suna bada hadin kai wajen gudanar da binciken.
You must be logged in to post a comment Login