Labarai
Ana tsaka da zaman majalisar zartarwa ta kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron Majalisar zartarwa a karo na bakwai ta kafar Internet a fadar Gwamnatin dake Vill a babban birnin tarayya Abuja.
Sai dai zaman na wannan karon a na sa ran ministan sufurin jiragen sama da ministan ilimi da kuma na gidadje za su gabatar da jawabai a ya yin taron.
Taron Majalisar dai ya hadar da mataimakain shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da sakataren Gwamnatin tarayya Boss Mustapha da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati Farfesa Ibrahim Gambari da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno.
Buhari zai rabawa manoma bashi- Sabo Nanono
Buhari, Zulum, Kwankwaso, El-Rufai- Wa Nigeria ta fi bukata a cikinsu?
Kazalika rahotanni na bayyana cewa yan Majalisar zartarwar za su halarci taro ne ta kafar sadarwa a ofisoshin su ciki har da ministan shari’a Abubakar Malami.
Kazalika akwai ministar kasafi da tsare tsare Hajiya Zainab Ahmad da ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika da na ayyuka na musamman George Akume da Lai Muhammad na tattabara bayanai da al’adu.
You must be logged in to post a comment Login