Kiwon Lafiya
Kwalara: Adadin rayukan da aka rasa sun zarta dubu 3
Cibiyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta ce, sama da mutane dubu 3, 449 ne suka mutu sakamakon cutar kwalara a 2021.
Rahoton na NCDC ya kuma bayyana cewa mutane sama da dubu ɗari da a hamsin da bakwai sun kamu da cutar a jihohi 32 har da birnin tarayya Abuja.
A cewar NCDC yaran da ke tsakanin shekara biyar zuwa 14 ne suka fi kamuwa da cutar tsakanin maza da mata, yayin da kashi 50 cikin 100 suka kasance maza ne.
Jihohin da aka samu bullar cutar kwalara a bana su ne Abia, Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano.
Sai Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Sokoto, Taraba, Yobe, Rivers, Zamfara da kuma birnin tarayya Abuja.
NCDC ta kuma ce, daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa 7 ga watan jihohi shida sun ba da rahoton sake ɓullar cutar guda 78 da suka hadar jihohin Borno 32, Kebbi 20, Adamawa 19, Cross River 3, sai Ogun 2 da jihar Oyo 2
You must be logged in to post a comment Login