Labarai
Ba siyasa ce zata sa mu shimfida layin dogo ba – Buhari
Gwamnatin tarayya ta ce bunkasar tattalin arzikin kasar nan shi ne dalilin da ya sanya ta ke kokarin shimfida layin dogo daga Kano zuwa Maradi a jamhuriyar Nijar, ba batun siyasa ba kamar yadda wasu ke yadawa.
Ministan sifiri Rotimi Amaechi ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai jiya a Abuja.
Ya ce, ba daidai bane wasu al’ummar kasar nan su rika sa batun siyasa cikin aikin da ya ce ba shakka zai taimaka wajen bunkasar tattalin arzikin Najeriya.
Rotimi Amaechi ya ce ba ya ga samar da aikin yi, jirgin kasar zai kuma taimaka wajen bunkasa shige da ficen kayayyaki tsakanin kasashen biyu.
Ministan sifirin ya kara da cewa, gwamnatin ta dau wannan mataki ne biyo bayan nazartar yadda ake samun gasa tsakanin tashoshin jiragen ruwa da ke makwabtaka da kasar nan.
Har ma ya buga misalin cewa musamman na jamhuriyar Benin da Togo da kuma Ghana, wanda shimfida layin dogon zai sa ‘yan kasuwar Nijar su karkatar da akalar kayayyakinsu zuwa tashoshin jiragen ruwan Najeriya.
AI
You must be logged in to post a comment Login