Labarai
Badaru ya biya ‘yan Fanshon Jigawa hakkin su
Gwamnatin jihar Jigawa a Nigeriya ta ce duk wani ma’aikacin ta da lokacin barin aikin shi ya yi, to ya yi gaggawar shigar da bayanan shi ga hukumar domin karbar hakkin sa na fansho.
Shugaban hukumar a jihar Hashim Ahmad Fagam ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Dutsan jihar a ranar 31 ga watan Agusta shekarar 2021.
Ya ce gwamnati ta biya hakkin ‘yan fanshon da suka bar aiki a watan Yulin wannan shekara kudaden su da ya kai sama da Naira Tiriliyon daya da rabi.
Gwamnatin Jigawa ta rabawa jama’a Awaki domin kiwo
Ya kara da cewa sun bawa iyalan ma’aikatan da suka rasu hakkin su da ya kai sama da Naira miliyan dari biyu da casa’in da biyar.
Hashim Ahmad Fagam ya kara da cewa a yanzu babu wani dan fansho a jihar ta Jigawa da kebin gwamnati hakkin shi da ba’a bashi bah.
You must be logged in to post a comment Login