Labaran Wasanni
Brazil na tattaunawa da PSG akan dan wasa Neymar
Hukumar kwallon kafa ta kasar Brazil, CBF, ta fara tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain, don cimma matsayar dan wasan ya jagoranci tawagar kasar a gasar wasannin motsa jiki na bazara wato Olympic a birnin Tokyo na kasar Japanda zai gudana a shekarar bana.
Dan wasa Neymar, na daga cikin tawagar kasar sa a matsayin ‘yan wasa guda uku da aka kayyade shekarun sun da suka haura ashirin da uku da ake bada dama ga kasashe da su yi amfani dasu a cikin tawagar su da suka wakilci kasar Brazil a gasar da a ka kammala a birnin Rio na kasar Brazil shekarar 2016, wanda Brazil suka dauki lambar zinare.
Labarai masu alaka
An sayi dan wasan Dambe naira dubu hudu a Kano
Za’a kece raini tsakanin Man City da Madrid
Dan wasa Neymar, ya nuna sha’awar sa ta wakiltar kasar sa a gasar cin kofin nahiyar Amurka wato Copa America, da zai gudana a kasar Columbia, da ga ranar sha biyun ga watan yuni a kuma karkare sha biyu ga watan yuli, wanda da zarar an kammala shi zai zama kwana goma tsakanin su da fara gasar wasannin Olympic.
‘Yan wasa da suka hada da Vinicius Junior da Rodrygo da Reinier da sabon dan wasan kungiyar Lyon ta kasar Faransa, Bruno Guimarães na daga cikin ‘yan wasan da ake sa ran zasu wakilci Brazil a gasar.
Kasashe goma sha shida, 16 , ne zasu fafata a wasan kwallon kafa na maza, har da mai masaukin baki kasar Japan.
You must be logged in to post a comment Login