Labaran Kano
Buhari ya ce a gobe Talata za’a kaddamar da shirin daukar ma’aikata
A gobe talata ne gwamnatin Najeriya za ta kaddamar da shirin daukar ma’aikatan wucin gadi dubu dari 7 da 74 a fadin kasar.
Karo na 3 kenan ana dakatar da shirin.
A shafinsa na tuwita karamin Ministan Kwadago da samar da ayyuka na kasar Festus Keyamo,ya ce an kammala dukkan shirye-shirye na kaddamar da daukar ma’aikatan, kuma za’a dauki mutum dubu 1 a kowacce karamar hukuma dake kasar nan.
Za’a biya naira dubu 20 a matsayin alawus ga ma’aikatan wucin gadin a kowanne wata, tsawon watanni 3 da za’ayi ana shirin.
You must be logged in to post a comment Login