Labaran Wasanni
CAF: An rage dakatarwar da aka yiwa Austin Oladapo
Kwamitin daukaka a kan al’amuran wasannin gasar confederation Cup ta Afrika, ya ragewa kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Enyimba, Austin Oladapo dakatarwar da akai masa daga shiga dukkan al’amuran gasar daga shekara 1 zuwa watanni 6.
Hukumar kwallon kafa ta Afrika Caf a baya ta dakatar da dan wasan na tsahon shekara daya, dalilin da ya sanya kenan kungiyar ta shigar da kara gaban kwamitin haka yasa aka rage zuwa watanni 6.
Muna bukatar bayanin rashin kokarin ‘yan wasan Najeriya a Tokyo 2020-Reps
Ana karar dan wasan na Enyimba da yin gwajin annobar covid 19 ta Bogi.
Haka zalika bayan an dakatar dashi daga wasa dan wasan ya sake bugawa kungiyar wasa na 2 a gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrikan a Nigeria.
Kwamitin ya kuma ce kungiyar za ta rubutowa jami’an kula da lafiya na hukumar takardar neman afuwa bisa karyata jami’in lafiya da dan wasan ya yi a gaban jama’a, wanda dan wasan ya ringa cewa jami’in bai san aikinsa ba.
A Ranar 4 ga watan Janairun shekara ta 2022 ne dan wasan zai dawo ci gaba da bugawa kungiyar ta Enyimba wasa.
You must be logged in to post a comment Login