Coronavirus
Corona ta tarwatsa kwamitin yaki da ita na Kano

Rahotonni daga Kano na cewa izuwa yanzu an samu karin mutane 6 da suka kamu da curar Coronavirus.
Wata majiya mai tsuhe ta shaidawa Freedom Radio cewa mutane 6 da suka kamu, dukkansu na cikin kwamitin kar ta kwana na yaki da cutar a Kano.
Rahotonni sun ce yanzu haka ana cigaba da yiwa wasu gwaji, domin tabbatar da lafiyar su.
Har ila yau, majiyar ta shaidawa Freedom Radio cewa yanzu haka mutane 6 sun kama hanyar zuwa makillata a asibitin Muhammadu Buhari dake Giginyu wanda aka mayar da shi wurin killacewa kafin fara amfani da wurin killacewa na Kofar Mata.
You must be logged in to post a comment Login