Labaran Wasanni
Covid-19: An dakatar da kwallon kafa a Kano saboda Coronavirus
Tun bayan sanarwar da hukumar Kwallon kafa ta Kasa (NFF) ta fitar na dakatar da dukkan wasannin Kwallon kafa a kasar nan, sakamakon cutar Coronavirus, kungiyoyin Kwallon kafa a jihohin kasar nan, na bin umarnin sau da kafa, ciki har da hukumar Kwallon kafa ta jihar Kano.
A wata sanarwa, da sakataren hukumar ta jihar Kano Alhaji Shehu Buhari ya sakawa hannu, ta umarci dukkanin hukumomin Kwallon kafa na kananan hukumomin jihar 44, da su dakatar da komai ba gudanar da wasanni har zuwa abinda hali ya yi na yadda aka tunkari cutar ta Corona ko kuma shawo kan yaduwar ta.
Jim kadan, bayan fitar da sanarwar, kungiyoyi da dama da suka hadar da Kano Pillars, ta bakin kakakin ta Rilwanu Idris Malikawa, ta sanar da bin dokar sau da kafa tare da umartar ‘yan wasan kungiyar da su tafi hutu.
Haka ita ma kungiyar Kwallon kafa ta Ramcy Fc, dake gidan Sarki, ta bada umarnin bin dokar tare da tsaida atisaye da tura ‘yan wasanta hutu zuwa abinda hali ya yiwu, a ta bakin jami’in yada labaranta Aminu Abba Kwaru.
Karin labarai:
Kano Pillars ta lallasa Jigawa Golden Stars
Kano Pillars ta lallasa Delta Force da ci 6-1
A bangare daya, kuma hukumar Kwallon kafa ta Tarauni, ta bakin Sakataren ta Isma’il Fango, da kakakin ta Rufa’i Bateza Unguwa uku, sun sanar da dakatar da komai da ya shafi Kwallon kafa a karamar hukumar har sai an ga yadda ta yiwu dangane da barazanar cutar ta Covid-19.
Zuwa yanzu dai a iya cewa, harkokin Kwallon kafa a fadin jihar Kano, birni da kauyuka sun tsaya cik, sakamakon bin umarnin hukumar Kwallon kafa ta jiha karkashin jagorancin Sharif Rabiu Inuwa Ahlan, wadda ita ma ta karbi umarnin dakatarwar daga hukumar Kwallon kafa ta Kasa karkashin Mista Amaju Melvin Pinnick.
A ‘yan kwanakin nan, harkokin Kwallon kafa a duniya ya samu tsaiko, sakamakon bullar cutar ta Corona Virus, dake kara yaduwa a fadin duniya, inda manyan kasashe masu dumbin magoya baya da kuma manyan kungiyo dake taka Leda, da suka hada da Italiya, Faransa, Jamus(Germany ) Andalus(Spain) da kasar Ingila suka dage wasannin gasar kakar kasashen su bisa bullar cutar a kasashen.
You must be logged in to post a comment Login