Labarai
Covid -19 Ba za’a rage albashin ‘yan wasan firimiya ta kasa ba
Kungiyoyin dake buga gasar Firimiya ta kasa zasu cigaba da karbar albashin su ba tare da zabtare ko rage wani kaso a cikin sa ba kamar yadda aka dinga rade radi a baya.
Rahotanni a baya na ta kewaya wa cewar akwai yiwuwar zabtare albashin wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyoyin dake taka leda a kasar nan, tun bayan bullar cutar Corona Virus, a fadin duniya wanda hakan ya sa wasu kungiyoyi da ‘yan wasa da dama a nahiyar turai da sauran kasashe rage kudaden gudanar da su tare da rage yawan ma’aikata duba da halin da ke ciki.
Labarai masu alaka.
An fidda alkaluman gasar firimiya ta kasa zuwa wasannin mako na ashirin da biyu
Anyi garkuwa da ‘yan wasa biyu a Firimiyar Najeriya
Hakan tasa ‘yan wasa a kasar nan fargabar rage musu albashi kasancewar mafiya yawan kungiyoyin gwamnatocin jihohi ne ke daukar nauyin su.
A baya dai kungiyar kwallon kafa ta Yobe Desert Stars, ta rage yawan alabashin ‘yan wasanta dana ma’aikatan kungiyar da kaso saba’in da biyar cikin dari.
You must be logged in to post a comment Login