Labarai
Dalilan da zai sanya a sake yin nazarin komawa makarantu a Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta ce, zata sake yin nazari kan komawa makarantu da za’a yi a ranar 18 ga watan Janairun ne, kasancewar ana yawan samun karuwar masu dauke da cutar Korona a kasar nan a kullum.
Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ne ya bayyana hakan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ya yin zaman kwamitin shugaban kasa kan yaki da cutar Corona.
Malam Adamu Adamu ya danganta wannan matakin da gwamnati zata dauka na sake yin nazarin komawa makarantu a kasar nan da dawowar cutar Corona a karo na biyu wanda ake fama da shi a Najeriya a halin yanzu da ma duniya baki daya.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, Ministan Ilimin na cewa, bude makarantu a wannan lokacin bai dace ba, la’akari da yadda adadin masu dauke da cutar ke karuwa a kullum wanda hakan ke sanya fargaba a zukantan ‘yan Najeriya.
Corona : Yau dalibai ke shiga mako na biyu da komawa makaranta a Kano
Buhari ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji yiwa kan su gwajin Corona
Freedom Rediyo wata makaranta ce mai zaman kanta – Ambasada Sani Bala
Akan haka ne Malam Adamu Adamu ya ce gwamnati ta yanke shawarar komawa makarantun ne a ranar 18 ga wannan wata a matsayin gwaji ko kuma manufa da aka tsara don cimma nasara.
Sai dai ya ce Gwamanati na kula da abubuwan da ke afkowa a cikin al’umma, a don haka ya zama wajibi a sake yin nazari kan komawa makarantu a Najeriya
You must be logged in to post a comment Login