Coronavirus
Covid 19: gwamnati bata bawa kamfanoni damar shigo da allurar rigakafi ba
Gwamnatin Tarayya ta ce ba ta ba da izinin shigo da alluran rigakafin COVID-19 daga kamfanonin masu zaman kan su zuwa kasar nan ba.
Ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire ne ya bayyana hakan ne a yayin taron kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da cutar corona wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, ba a ba da izinin shigo da alluran COVID-19 daga kamfanoni masu zaman kansu ba saboda rahotannin da ake samu na samar da alluran marasa inganci.
Da yake magana kan batun ingancin allurar rigakafin ta Astrazeneca kuwa ministan ya sake ba da tabbacin cewa alluran na da inganci kuma bata da wata illa ga wadanda aka yiwa a kasar nan.
Dakta Osagie Ehanire ya kuma ce, tuni shugaban kasa da mataimakinsa da sauran shugabannin kasa suka karbi allurar rigakafin kuma a yanzu haka suna cikin koshin lafiya.
A cewar sa tuni hukumar kula da inganci abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta samar da wata hanya da za a aike mata sako musamman ga wadanda suka karbi rigakafin corona suka suskanci matsala.
You must be logged in to post a comment Login