Coronavirus
Covid-19: Gwamnati ta bada damar cigaba da sufuri a Nijar
A dazu-dazun nan ne a yayin zaman majalisar ministoci da shugaba Isufu Mahamadu ya jagoranta gwamnatin Nijar ta bayyana matakinta na janye dokar hana jigila a fadin kasar baki daya.
Gwamnatin ta ce sakamakon cigaba da ake samu cikin yaki da cutar Covid-19 ne yasa ta dauki wannan mataki.
Wakilinmu Yakuba Umaru Maigizawa ya rawaito mana cewa baya ga wannan ma gwamnatin ta ce daga yanzu kofar babban birnin Yamai za ta kasance a bude bayan killace birnin na tsahon lokaci saboda Corona.
Dama dai al’umma na zaman jiran wannan mataki biyo bayan bude wuraren ibada da na sanar da ranar komawa makarantun boko a baya bayannan.
Tuni dai wasu manyan kamfanonin motocin masu sufiri a kasar da ma ketare suka fara fitar da sanarwar cigaba da ayyukansu.
You must be logged in to post a comment Login