Coronavirus
Covid-19: Mawadata su tallafawa wadan da basu dashi- HOLPI
Kungiyar Tallafawa Marayu da marasa karfi wato Hope for Orphans and Less Privileged Initiative (HOLPI) ta jaddada kudirin ta na ci gaba da tallafawa mabukatan da suke neman taimako musamman a wannan lokaci na Azumin watan Ramadan da kuma zaman gida da al’umma kanyi sanadiyyar annobar Corona.
A satin daya gabata ne dai kungiyar ta raba kayan abinci ga iyayen marayu dake kananan hukumomin uku a nan jihar Kano.
Kananan hukumomin da kungiyar ta rabawa tallafin sun hadar da karamar hukumar Tarauni da Tofa da kuma Dawakin Tofa.
Da take jawabi jim kadan bayan mika tallafin ga mabukatan shugabar kungiyar ta HOLPI, Hajiya Bilkisu Sani Yola, ta ce sun raba tallafin ne ga mabukatan dake kananan hukumomin, bayan zabo wadan da ke da bukatar a tallafa musu bisa halin da suke ciki na babu.
Hajiya Bilkisu Sani Yola, ta kuma ce ‘ya’yan kungiyar ta HOLPI na yin karo-karo ne ga membomin ta a dukkanin karshen wata da kuma iyayen kungiyar tare da dai-daikun mutane don tallafawa wadan da basu dashi.
Ta kuma ce da fari sun shirya tallafawa magidantan da basu dashi guda dari ne da kayan abinci, amma da suka fara gudanar da rabon a kananan hukumomin sun rabawa sama da magidanta Dari biyu da tallafin kayan abinci don rage musu radadin da suke ciki na halin babu.
Hajiya Bilkisu Sani Yola ta kuma yi kira ga mawadata da dai-daikun mutane da su rinka tallafawa wadan da basu dashi musamman a wannan lokaci da ake ciki na annobar Corona data tilastawa mutane zaman gida.
Covid-19: Ganduje zai fara raba tallafin kayan abinci
Covid -19:Kungiyar likitocin dabbobi ta bada tallafi
Wasu daga cikin mutanan da suka amfana da tallafin da suka fito daga kananan hukumomin na Tarauni da Tofa da Dawakin Tofa wadan da suka hadar da Muhammadu Sani da Malama Hafsat sun bayyana farin cikin su tare da godewa kungiyar bisa basu tallafin da tai.
Kayan da kungiyar ta HOLPI ta raba ga mabukatan a kananan hukumomin sun hadar da Shinkafa da Wake da Madara da Sikari da Taliya da Makaroni da Gero da Sabulu da Tumatir da dai sauran kayan abinci dana bukatar yau da kullin.
Mai magana da yawun kungiyar Kwamred Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba ga manema labarai a ranar shida Mayun da muke ciki.
You must be logged in to post a comment Login