Labarai
COVID-19 : Tambuwal ya dakatar da bajakolin nuna al’adu
Gwamnatin jihar Sokoto ta datakatar da baje kolin nuna kayayyakin al’adun gargajiya da shirya yi a yau Laraba.
Gwmnan jihar Sokoto Allhaji Aminu Waziri Tambuwal ya sanar da hakan ta bakin kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Alhaji Bashir Gidado ya yin da yake ganawa da manema labarai a cibiyar bajakolin na jihar.
Alhaji Bashir Gidado ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakin ne da nufin dakile cutar Coronavirus a jihar ta Sokoto kasancewar cutar ta zama Annoba a duniya baki daya.
Kwamshinan ya nuna takaicin sa kan dakatar da bajakolin amma kuma ya ce jihar bata da mafita illa kawai ta dauki matakin dakatar da bajakolin ya yin da ake daf da kaddamar da shi a yau ganin yadda aka sami karuwar masu dauke da cutar ta COVID-19 a duniya da ma Najeriya baki daya.
Mun yi wa ma’aikatan bogi tayin afuwa -Tambuwal
Shekara daya da rasuwar Shagari: Irin ayyukan da yayi wa Najeriya.
INEC SOKOTO:Gwamna Tambuwal ya ce basu amince da ayyana zaben jihar bai kammala ba
Idan za’a iya tunawa dai, A jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da kaddmar da bukukuwan wasannin na kasa wanda aka shirya yin sa a jihar Edo tun da fari da kuma sansanin horar da ‘yan hidimar kasa baki daya na kasar sanan don kaucewa yaduwa da cutar ta Coronavirus.
You must be logged in to post a comment Login