Labaran Kano
Covid 19: Zamu bada taimako a jihar Kano-Dakta Sani Yahaya
Wani Babban Jami’in Banki Mai kula da shiyyar Arewa ma so yamma, Dakta Sani Yahaya , yace bankin zai bada tallafin kayan taimako na yaki da cutar Corona na miliyoyin Nairori ga gwamnatin jihar Kano, a yunkurin da ake na dakile cutar dake Addabar kasashen duniya, ciki har da wasu jihohin kasar nan.
Dakta Sani Yahaya, ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai daya gudana , da Bankin yake bayyana kalubalen da suke fama dashi na abokanan hulda sakamakon halin da ake ciki na killace Kai da takaita zirga-zirga da mu’amala tsakanin al’Umma.
Sani Yahya, ya kara dacewa akwai matakai da suke dauka na killace abokan hulda, da takaita yawan wadan da zasu yi mu’amala a ranakun aiki, tare da samar da sinadarin wankewa da tsaftace hannu a na’urar in jin cire kudi wato ATM,don Lura da lafiyar al’Umma.
Labarai masu alaka.
Covid19: Bankin CBN ya bayyana ka’idojin bayar da tallafi
Shugaba Buhari ya bukaci gudunmuwar bankin musulunci don bunkasa rayuwa
Babban Jami’in ya kara dacewa, sabanin yadda al’umma suke ikirari na cewar ba a kulawa dasu da kin bude bankuna, su ne daga bangaren bankuna suke fuskantar kalubale da tirjiya daga abokan hulda kasancewar basa son yin amfani da sindarin wanke hannu da kin bin dokokin yadda za’a kare kai don kaucewa kamuwa da cutar.
Jami’in Bankin yace zuwa yanzu haka, Bankin ya bada sama biliyan biyu a fadin kasar nan da jiha a yakin da hukumomi suke na dakile cutar a fadin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login