Coronavirus
Covid19: Badaru ya bada umarnin rufe karin kananan hukumomi hudu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara sanya dokar zaman gida na tsawon mako guda wadda dokar zata fara daga karfe 12 na daran ranar Juma’a, a kananan hukumomi guda hudu, samakon samun Karin mutanen da suka kamu da cutar COVID-19.
Kana nan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Dutse da Gwaram sai Auyo da kuma karamar Hukumar miga.
Shugaban kwamatin yaki da yaduwar cutar kuma kwamin shinan lafiya na jihar jigawa Dr. Abba Umar ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.
Kwamin shinan ya kara da cewa guda cikin wadan nan mutane biyar da suka kamu da wannan cuta tini ya rigamu gidan gaski, sakamakon zafin da cutar tayi jikinsa kafin kaishi asibiti asibiti don bashi kulawa data kamata.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito kwamin shinan na cewa mafi yawan mutanan sunzo da cutar daga gurin cirani, ba wai wani ya dauka a gurin wanine cikin jihar.
Karin labarai:
BUK zata fara gwajin masu dauke da cutar Corona
Gwamna Badaru ya tsawaita “Lock Down” a garin Kazaure
Ya zuwa yanzu dai mutane 9 cutar ta kama a jihar jigawa ciki hadda wanda jahar kano ta maidawa jigawa, wadda tini kwamin shinan yace gwamnati ta fara duba yadda zata temaki masu karamin karfi a wannan yankuna kafin rufewa.
Wannan dai na zuwane a kwana guda da sanya dokar zaman gida a garuruwan Birnin kudu da Gumel sai kuma gujungu c ta karamar Hukumar Taura, wanda sokar zata fara aiki da karfe 12 daran ranar alhamis dinnan.
You must be logged in to post a comment Login