Labarai
Covid19: Bankin CBN ya bayyana ka’idojin bayar da tallafi
Babban bankin kasa CBN ya bayyana wasu ka’dojin da mutane ko kamfanoni za su cika kafin cin gajiyar tallafin naira biliyan hamsin da ya ware domin rage radadin cutar Corona.
A makon jiya ne dai bankin na CBN ya sanar da ware kudaden sakamakon ci gaba da yaduwar cutar ta Covid-19 wanda ya yi illa ga tattalin arzikin kasar nan.
Bankin ya ce, kudaden na tallafi ne wanda zai ragewa al’ummar kasar nan radadi da kuma asarar da suka tabka sakamakon cutar ta Corona.
A cewar babban bankin kasa CBN wadanda za su ci gajiyar tallafin za su kasance magidanta ne da kuma suke gudanar da wasu sana’oi wanda suka samu koma baya sakamakon ci gaba da yaduwar cutar Corona.
LABARAI MASU ALAKA
Covid-19: Najeriya za ta iya samun durkushewar tattalin arziki
Da dumi-dumi Gwamnan jihar Bauchi ya kamu da COVID-19
Ganduje : zan yi duk mai yuwa wajen hana COVID-19 shigowa Kano
Haka zalika suma masu masana’antu da suke da hujja kwarara da suka nuna cewa cutar Corona ta yi illa ga harkokinsu suna cikin wadanda za su samu tallafin.
Ta cikin sanarwar na CBN dai, masu harkar noma ko masu harkokin Otel da samar da abinci da harkokin lafiya da kuma masu harkokin sifirin jiragen sama wadanda suke da hujjoji na asara sakamakon cutar ta Corona suna cikin wadanda za su ci gajiyar kudaden.
Sai dai bankin na CBN ya kuma ce, magidanta da ke da kananan sana’oi za su iya cin gajiyar kudin da bai wuce naira miliyan uku ba.
You must be logged in to post a comment Login