Manyan Labarai
Cutar Corona na yaduwa kamar wutar daji a kasashen Afrika – WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar Corona na saurin yaduwa a kasashen Afrika kamar wutar daji, yayin da a gefe guda kuma ake samun yawan wadanda suke mutuwa sakamakon cutar.
Sai dai WHO ta ce tana duba kasar ta cutar tafi shafa a cikin kasashen duniya da annobar ta yi Kamari don kai musu dauki.
Idan aka yi duba da yawan wadanda suka kamu kuwa da cutar ta COVID-19, a halin yanzu a kasashehin Afrika wadanda suka kamun basu da yawa idan aka kwatanta da na kasashen turai da ma duniya baki daya,
Da dumi-dumi: Daukacin masu Corona sun warke a Jigawa
Mai Corona daya ne ya rage a jihar Jigawa
Masu cutar Corona 11,828 sun warke a Najeriya
Amma kuma yawan wadanda suka kamu da cutar na bazuwa a wasu kasashen wanda hakan ke janyo hankulan hukumomin kiwon lafiya.
A cewar, WHO din nan da kwanaki 20 masu zuwa, kasashen Afrika za’a sami yawan masu dauke da cutar.
You must be logged in to post a comment Login