Labaran Wasanni
Dan wasan Liverpool Thiago Alcantara ya kamu da Corona

Dan wasan tsakiyar kungiyar Liverpool, Thiago Alcantara ya kamu da cutar Corona.
Dan wasan mai shekaru 29, yanzu haka ya killace kansa a gida kamar yadda dokar ta tanada.
Yanzu haka ba zai doka wasan da za su fafata da Lincoln a gasar EFL, sannan bai doka wasan da suka lallasa Arsenal da ci 3-1 a gasar Firimiya da suka fafata a makon nan.
You must be logged in to post a comment Login