Manyan Labarai
Ficewar Salihu Takai asara ce ga PRP – Dr. Dukawa
Masani akan al’amuran siyasar nan, Dakta Sa’idu Ahmad Dukawa na jami’ar Bayero dake nan Kano ya ce, babu dadi matuka sauyin shekar da ‘dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar PRP Malam Salihu Sagir Takai zai yi daga jam’iyyar ta PRP.
Yayin zantawar da yayi da shirin “An Tashi Lafiya” na Freedom Radio, Dr. Dukawa ya ce, asara ce babba ga jam’iyyar PRP idan Malam Salihu Takai ya fice daga cikin ta, sai dai ya ce akwai wasu abubuwan dubawa guda uku game da irin wadannan sauyin shekar.
Na farko, shi ne ‘yanci, kowa yana da ‘yanci yayi ra’ayin da yake so, ya shiga jam’iyyar da ya ga dama, ya fita daga wadda ya ga dama.
Karin labarai:
Na shirya ficewa daga jam’iyyar PRP – Salihu TakaiAbu na biyu kuma shi ne doka, babu wata doka da aka sabawa don an fita daga jam’iyya kaza zuwa kaza.
Abu na uku kuwa shi ne akida, ya kamata a ce kowace jam’iyya an gina ta ne saboda wata sananniyar akida, to wanda duk ya shiga PRP za a dauka yana da akidar ceton talakawa, amma fita daga PRP a shiga wata jam’iyyar a nan sai an tsaya an ga wacce mutum ya shiga.
A ranar Talata ne daraktan yakin neman zaben Malam Salihu Takai, Barista Faruk Iya Sambo, ya shaidawa shirin “Kowane Gauta” na nan Freedom Radio cewa, yanzu haka sun tattauna da magoya bayan su na kananan hukumomi 44 da sauran masu ruwa da tsaki, don cimma matsaya kan jam’iyyar da zasu koma.
Karin labarai:
Siyasar Kano: Ko ina makomar siyasar Malam Salihu Takai?
A shekara ta 2011 ne dai Malam Salihu Takai yayi takarar gwamna a jam’iyyar ANPP mai mulki a wancan lokaci, wanda bai samu nasara ba.
Haka ma a shekarar 2015 Takai yayi takara a jam’iyyar PDP, inda gwamna Abdullahi Ganduje ya kayar da shi a zaben.
A kakar zaben shekara ta 2019, Takai yayi takara a jam’iyyar PRP wanda ya zo na uku a zaben, zaben da ya baiwa gwamna Ganduje damar komawa karagar mulki a zagaye na biyu.
You must be logged in to post a comment Login