Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Garzali Miko yayi kaura daga Kano

Published

on

Fitaccen jarumi kuma Mawaki Garzali Miko, ya koma garin Azare na jihar Bauchi domin cigaba da gudanar da ayyukansa na fina-finai da waka.

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunan ta, shaidawa Freedom Radio cewa jarumin ya kai akalla wata guda da kwashe kayan sa daga garin Kano, inda ya koma garin Azare da zama.

Cibiyar horas da harkar fim ta bullo da hanyoyin bunkasa sana’ar

Akwai karancin ilimin harkar fim ga masu shirya fina-finai

Halin da ake ciki a Kannywood a wannan mako

Ana zargin dai Garzali Miko ya kauracewa Kano ne saboda tsoron sanya ido daga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano.

 

Miko dai na daya daga cikin jaruman da tauraruwar sa ke haskawa a wannan karnin.

Har ila yau, a ranar Asabar din da ta gabata ne, Garzali ya bude wani sabon gidan wasa a can garin na Azare, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!