Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta ce ruwan famfo zai dawo cikin birni kafin ƙarshen shekara

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce tana sa ran dawo da ruwan famfo a cikin birnin Kano kafin ƙarshen wannan shekara.

Kwamishinan Muhalli, Ruwa da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai domin duba aikin gyaran tashoshin samar da ruwa na Challawa da Tamburawa.

Ya ce ana ci gaba da gyaran matatar ruwan Challawa da kuma rumbun ajiyar ruwa na Goron Dutse, tare da shirin fara gwajin tsarin samar da ruwa a wasu sassan birnin.

A cewar kwamishinan, aikin na gudana ne a matakai, saboda ba za a iya magance dukkan matsalolin da suka shafi samar da ruwan a lokaci guda ba.

Dakta Dahiru ya ce gwamnatin jihar za ta gyara muhimman kayan aikin da suka lalace, domin kauce wa sake fuskantar matsalar karancin ruwa bayan kammala gyaran.

Ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da sa ido kan aikin, tare da tabbatar da cewa hukumomi da masu ruwa da tsaki da ke da alhakin samar da ruwan sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Gwamnatin ta ce burinta shi ne ganin al’ummar Kano sun samu wadataccen ruwan famfo.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!