Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Bayan sanar da sakamakon zabe: Gwamnatin Ganduje ta sanya dokar takaita zirga-zirga

Published

on

Bayan ayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya samu nasara, Gwamnatin jihar Kano, ta sanya dokar hana fita daga safiyar yau Litinin.

Gwamnatin ta sanya dokar ne ta cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Malam Muhammad Garba, ya fitar da safiyar Litinin din nan.

Sanarwar ta ce, an sanya dokar ne domin dakile yunkurin tayar da tarzoma bayan bayyana sakamakon zaɓen gwamna.

Haka kuma ta cikin sanarwar, gwamnatin jihar Kano, ta bukaci al’ummar jihar da su kasance masu rungumar zaman lafiya, ta hanyar kaurace wa duk wata fitina.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!