Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje zai hada hannu da Amurka wajen yakar cutuka masu yaduwa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce a shirye take domin hada gwiwa da kungiyoyi masu zaman kansu domin yakar cutuka masu yaduwa anan Kano.

Mataimakin gwamnan Kano Nasir Yusif Gawuna ya bayyana hakan  jim kadan bayan kaddamar da cibiyar gudanarwar gaggawa domin yakar cutuka masu yaduwa a asibitin Zana dake nan Kano da aka daga likafar ta da hadin gwiwar gwamnatin Amurka.

Ya Kara da cewa wannan cibiya zata taimaka wajen taimakawa jami’an lafiya domin tattara bayanai akan cutuka da kuma samun hanyoyin yadda za’a shawo kansu.

Labarai masu alaka : 

Ganduje ya nada sabon shugaban hukumar tattara haraji ta Kano

Majalisar dokoki ta bukaci Ganduje ya magance matsalar ruwa a Kano

Mataimakin gwamnan na Kano ya Kara da cewa bambamcin wannan cibiyar da ta Asibitin Nassarawa shi ne ita ana kafata ne domin kula da harkoki da suka danganci polio yayin da ita kuma wannan ta Asibitin Zana zata kasance ne babbar cibiyar kula da cutuka masu yaduwa.

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa taron da akayi ta kafar internet da jakadar Amurka a Nigeria Ambassador Mary Beth Leonard ya samu halartar kwamishinan lafiya na jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!