Labarai
Gwamnatin Masari ta ayyana gobe Alhamis a matsayin ranar hutu ga ma’aikata
Gwamnatin jihar Katsina, ta ayyana gobe Alhamis 26 ga Janairu a matsayin ranar hutun ma’aikata a dukkanin kananan hukumomin jihar domin shirin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hakan na cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar noma da walwalar jama’a Alhaji Sani Kabomo ya fitar ga manema labarai a yau Laraba.
Ya ce, an bai wa ma’aikata hutun ne domin su yi shirin tarbar shugaba Buhari da zai kai ziyara jihar domin kaddamar da wasu ayyuka da gwamnan jihar Aminu Bello Masarai ya samar.
Sai dai ya ce, hutun bai shafi wadanda suke aiki karkashin gwamnatin tarayya ba, da bankuna har ma da masu ayyuka na musamman.
You must be logged in to post a comment Login