Kiwon Lafiya
Hisbah ta gano maganin Coronavirus
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta gano maganin cutar Coronavirus da ta addabi al’umma a sassa daban-daban na duniya.
Babban kwamandan hukumar Hisbah Sheikh Muhammad Haroun Ibn Sina ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifan sauti mai tsawon mintuna biyar da ya wallafa ta shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
Ibn Sina ya ce, babban maganin cutar Coronavirus shi ne komawa ga Allah ta hanyar neman gafararsa, yin istigfari da kuma yin riko sau da kafa da bautar Allah.
Wannan cuta tana daga cikin cutukan da manzon tsira Annabi (s.a.w) ke neman tsari da su, a cewar Ibn Sina.
Babban kwamandan ya ce, abinda ya jawo wannan cuta shi ne yawon sabon Allah da al’umma keyi, inda yace take dokokin Allah da jama’a keyi sun kai Allah ya jarrabemu da cuta ma fiye da Coronavirus.
Karin labarai:
Daliban Kano a Sudan sun nemi a dawo dasu gida saboda Coronavirus
Covid-19: Masana a Kano sun yi tsokaci kan Coronavirus
A karshe Sheikh Ibn Sina ya ja hankalin al’umma kan suyi watsi da duk wasu bayanai da ake yadawa, na cewa al’umma suyi amfani da Albasa ko Tafarnuwa da sunan maganin cutar ta Coronavirus.
A yanzu dai za a iya cewa hukumar Hisbah ta bi bayan sauran hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a kasar nan da suka shiga jan hankalin al’umma tun bayan bullar cutar ta Coronavirus a Najeriya.
Idan zaku iya tunawa dai, baya ga matakan da gwamnatin tarayya ta dauka kan cutar, ita ma gwamnatin jihar Kano ta samar da lambobin gaggawa da jama’a za su rika tuntuba a duk lokacin da suka ji alamomin cutar.
You must be logged in to post a comment Login