Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar zaɓen Kano ta soki tsarin yin zaɓe ta na’ura

Published

on

Farfesa Garba Ibrahim Sheka, shugaban hukumar zabe ta jihar Kano

Hukumar zaɓe ta jihar Kano ta soki yunƙurin majalisar dattijai na komawa yin zaɓe ta hanyar na’ura.

Shugaban hukumar Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce, amfani da na’urar ba zai magance maguɗin zaɓe ba.

“Idan har ana so a samu sauƙin maguɗin zaɓe to sai ma’aikatan zaɓen sun gyara halayensu” a cewarsa.

Farfesa Sheka ya kuma ce, rage yawan jam’iyyun siyasa abu ne da ya dace wanda zai kawo ci gaba a harkar zaɓe.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da majalisar dattijai ta buƙaci sauya tsarin zaɓen zuwa amfani da na’ura.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayin da yake kada kuri’a a wani zabe da ya gabata.

Yaya ƴan Najeriya ke kallon yunƙurin kawo sabon tsarin?
Kwamared Kabiru Sa’id Dakata shi ne daraktan cibiyar wayar da kan al’umma kan shugabanci na gari da tabbatar da adalci ta CAJA.

Ya ce, da kamar wuya a iya aiwatar da tsarin a nan kusa.

“Gaskiya bamu kai wannan matakin ba a siyasance, da zamu iya yin wannan a nan kusa, duba da yanayin ƙasar ta mu da babu abubuwa na more rayuwa” a cewarsa.

Dakata ya ƙara da cewa, bamu da wutar lantarki, haka shi kansa sabis na intanet babu tsayayye.

Sannan ƴan ƙasa basu gasgata waɗannan shugabanni ba balantana su gamsu da su.

Ya ce, da yawa daga cikin shugabannin nan ƙuri’un da suka samu a zaɓen fidda gwani sun ninka wanda suka samu a zaɓen du gari, kuma hakan na nuna maguɗi ƙarara.

Labarai masu alaka:

Siyasar Kano: Mahangar masana kan zaben kananan hukumomi

Rahoto : Ganduje zai kashe fiye da Naira biliyan 2 wajen zaben kananan hukumomin

Me ya ke faruwa a zaɓen Najeriya?

A tsawon shekarun da suka gabata akasarin ƴan Najeriya na son ayi zaɓe mai inganci sai dai kuma ana samun kura-kurai waɗanda ke kawo cikas a mafi yawan zaɓen da suka gabata.

Masu sanya idanu sun sha zargin zaɓen ƙasar da satar ƙuri’u, da tursasawa masu jefa ƙuri’a da sayen ƙuri’un har ma da aringizo.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!