Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

INEC ta sanar da ranar bai wa sabbin gwamnoni da ƴan majalisa

Published

on

Hukumar INEC ta sanar da ranakun da za ta bayar da takardar shaidar lashe zaɓe ga sabbin zababbun gwamnoni da yan majalisun jihohi da suka samu nasara a zaben bana.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kwamitinta na yada labarai da ilimantar da masu kada kuri’a Mista Festu Okoye.

Sanarwar, ta ce, sashe na 72 (1) na dokar zaben Najeriya ta 2022 ne ya dora wa hukumar alhakin bayar da takardar shaidar samun nasara lashe zabe ga zababbun yan takara a cikin kwanaki 14 da yin zaɓe.

INEC ta kara da cewa, yanzu haka ta sanya ranar Laraba 29 ga wannan watan da muke ciki na Maris da kuma 31 ga watan dai na Maris a matsayin ranakun bayar da takardun shaidar cin zaɓen.

Haka kuma, Sanarwar ta ce za a bayar da takardar shaidar cin zaben ne a harabar ofisoshin hukumar da ke faɗin jihohin da aka gudanar da zaben a bana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!