Connect with us

Manyan Labarai

Kai tsaye: An fara kama waɗanda suka kwashi “Palliatives” a Kaduna

Published

on

Haruna Ibrahim Idris

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta cafke wadanda ake zargi da fasa ofishin hukumar NAFDAC da ke unguwar Narayi a karamar hukumar Chukun.

Cikakken labarin zai zo a nan gaba.

Basheer Sharfadi

Har yanzu dokar hana fita na nan a Kaduna – El-rufai

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce, har yanzu ba ta sassauta dokar hana fita da ta sanya a jihar ba.

Gwamnatin jihar ta sanar a shafinta na Facebook cewa, idan akwai wani sauyi game da dokar to za a sanar a hukumance.

Sanarwar ta nemi jama'ar Kaduna da su ci gaba da biyayya ga dokar tare da bai wa jami'an tsaro haɗin kai don tabbatar da doka da oda.

A ranar Asabar ne wasu mazauna garin na Kaduna suka far wa ɗakunan ajiyar kayayyakin tallafin Corona.

Inda aka wawashe kayayyaki, wanda daga bisani gwamnatin jihar ta ce gurɓatattu ne ta kuma gargaɗi al'umma kan amfani da kayan.

Kan wannan ne kuma ta sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a jihar.

Auwal Hassan Fagge

Ganduje ya ɗage gabatar da kasafin kuɗin baɗi

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ɗage gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2021.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan ya sanar da cewa a ranar Litinin 26 ga watan Oktoban da muke ciki zai gabatar wa majalisa kasafin kuɗin.

A zaman majalisar dokokin na ranar Litinin shugaban majalisar Abdul'aziz Garba Gafasa ya gabatar da takardar da gwamna ya aiko, don neman gabatar da kasafin kudin a ranar Talata 27 ga watan Oktoba.

Wanda haka ke nuna gwamnan ya dage gabatarwa a ranar Litinin.

Sai dai gwamnatin Kano ba ta bayyana dalilin ɗage gabatar da kasafin kuɗin ba.

Basheer Sharfadi

Boka ya sanya wani matashi wanka da fitsari a Kano

Rundunar ƴan sanda ta cafke wani malami da ake zargin boka ne a unguwar Hotoro da ke nan Kano.

Ana zargin malamin ne da sanya wani matashi wanka da ruwan magani da aka cakuɗa da fitsari da kuma rubutun allo.

Matashin mai suna Kabiru Sani Sulaiman ya shaida wa Freedom cewa, ya je wajen Malamin ne domin neman yayi masa addu’a.

Sai dai daga baya ya nemi shi kan ya taimake shi cikin wani aiki da zai yi na samar da layar ɓata.

Malam Yahaya da ake zargi da bokanci.

Daga nan ne kuma sai ya bashi ruwan magani, da rubutu haɗi da fitsarinsa, domin yayi wanka da shi.

“Malam ya nemi na kawo dan ƴar uwata jaririn wata 10, domin a ciri idonsa ayi amfani dashi wajen hadar layar” a cewar Kabiru.

Samira Sani Sulaiman ita ce ‘yar uwar matashin ta ce hankalinta ya kaɗu matuƙa lokacin da ɗan uwanta ya zo mata da buƙatar.

To amma Malam Yahaya da ake zargi wanda dattijo ne mai shekaru 60 a duniya ya musanta.

Inda ya ce, ya shafe tsawon shekaru yana gudanar da sana’ar bayar da magunguna, kuma shi taimako kawai ya yiwa matashin.

Ƴan sanda sun sami malamin da wasu kayayyaki da suka haɗa da ƙasar duba da kuma hatimai gami da wasu abubuwa masu kama dana siddabaru.

Kakakin ƴan sandan jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, zuwa yanzu binciken su ya gano cewa malamin matsafi ne kuma zasu gurfanar da shi a gaban kotu.

Idan zaku iya tunawa a makon da ya gabata ma, rundunar ƴan sandan Kano ta cafke wani boka da ake zargi da hannu dumu-dumu wajen tunzura matarnan Hauwa’u Habib da ake zargi da hallaka ‘ya’yanta guda biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv

Now Streaming

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!