Labaran Wasanni
Kalubale ya hana ‘yan wasan Najeriya buga wasanni 100-Enyeama
Tsohon mai tsaran gida na Super Eagles Vincent Enyeama, ya alakanta rashin samun ‘yan wasannin kasar nan da gaza buga wasannin 100 ko sama da haka da matsalolin da ake fuskanta a tawagar ta Super Eagles.
Enyeama, yace rashin samun hadin kai da kuma fahimtar juna tsakanin ‘yan wasa da kuma jami’an kungiyoyi ne silar hakan.
A karshen watan Satumba za’a gudanar da zabe a hukumomin wasanni na Najeriya-Sunday Dare
A baya dai ‘yan wasa biyu ne a tawagar Super Eagles suka iya buga wasanni 100 a kungiyar da suka hada da shi kansa Enyeama da kuma Joseph Yobo.
‘Yan wasa biyun sun sami damar lashe gasar kofin nahiyar Afrika a shekarar
2013 da kasar Afrika ta kudu takarbi bakuncin gasar wanda Najeriya tayi galaba kan kasar Burkina Faso daci daya da nema, a wasan karshe.
Da ya ke ganawa da jaridar ESPN, tsohon mai tsaran gida na Enyimba yace indai ‘yan wasa irinsu Austin Okocha, Peter Rufai, Nwankwo Kanu da Mikel Obi da wasu ‘yan wasan basu samu damar haka ba lamarain ya zama abun dubawa.
“Buga wasanni 100 ba wani abu bane, nayi takaici ace ‘yan wasa biyu ne kawai a Super Eagles suka iya buga wadannan wasannin”
“Akalla muna da ‘yan wasa sama da 10 zuwa 15 a yanzu, amma babu wanda ya kai ga buga wasa 100 sabi da rashin tsayayyun masu horarwarwa a kungiyar” a cewar Enyeama
Ya kuma ce ‘yan wasa irinsu Jay Jay (Okocha), Peter Rufai, Mikel da Kanu sun cancanci ace sun buga wasanni 100, a Super Eagles.
You must be logged in to post a comment Login