Kasuwanci
Kamfanin TCN ta tallata gwanjon jirage masu saukar ungulu
Bayan shafe shekaru na halin ko in kula da kamfanin samar da wutar lantarki ta kasa ,wanda ta gada daga tsohowar kamfanin wutar lantarki NEPA na wasu jirage masu saukar ungulu guda hudu, wanda kudadensu ya kai kimanin dala dubu dari bakwai da ashiri kwatankwacen fiye da Naira miliyan dari biyu da hamsin da biyu, wanada za’a yi gwanjon su.
Jiragen mallakin hukumar samar da wutar lantarki ta sun bayyana kudirinsu na gwanjon wadannan jirage mai kirar BO-105 , da suke ajeye a filin jiragen saman na cikin gida dake Murtala Muhammad a jihar Lagos.
Jaridar Punch ta rawaito cewar jiragen saman masu saukar ungulu da ake amfani da su wajen kai kawon duba kayyakin wutar lantarki tare da aiwatar da wasu gyare-gyare a fadin kasar nan , suna nan zaune ne ba tare da ana amfani da su ba na tsawon lokaci.
Biyu daga cikin jiragen masu dauke da lamba 5N-ASK da 5N-ASJ rabon da suyi yi aiki tun a shekara ta 1995-1997, kuma an kira su ne a shekara 1978.
Kamfanin TCN ya ce wasu kwantenoninsa guda biyu sun yi batan dabo
Kamar yadda hukumar samar da wutar lantarkin ta ce, babu fa’ida na a gyara su, mai makon haka, kamata yayi a sayar da su a akan kudi dala dubu dari a halin da suke ciki.
Ragowar jiragen kuwa guda biyu masu lambar ta rijista 5N-BCj da 5N-EPA suna ajeye ne tun shekara ta 2008 kuma za’a iya sayar da su a kan kudade dala dubu dari uku da arbain da kuma dala dubu dari da tamanin.
Su kuma an kira su ne a shekara ta 1996 da kuma 1993 suma gyara wanda za’a iya gyara su domin suyi aiki amma na dan lokaci.
Hukumar dai a ‘yan kwanakin nan ne suka fitar da gayyatar masu saye domin su zo su saye.
A dai kwanakin baya ne tawagar gwamnati daga bangaren sharia suka je suka duba jiragen masu saukar ungulu a ranar Asabar din da ta gabata domin duba su kafin a fara gwanajan su.
Haka zalika Shugaban kwamitin majalisar datijjai dake kula da wutar lantarki sanata Yusuf Yusuf dake wakiltar Taraba ta tsakiya ya ce makasudin ziyarar shi ne domin duba lafiyar jiragen kafin a sayar da su.
Ya kara da cewa daga cikin abinda suka gani za’a yi iya gwanjon biyu daga cikin su , amma ragowar kuwa za’a iya sayar da su a matsayin ‘yan gwangwan