Wasanni
Kamaru ta fitar da Super Falcons a gasar WAFCON

Ƙungiyar kwallon ƙafar mata ta Kamaru, Indomitable Lionesses, ta fitar da zakarun gasar, Super Falcons ta Najeriya, daga gasar cin kofin Afrika ta mata ta 2026.
Kamaru ta doke Najeriya da ci ɗaya da nema a wasan kusa da na kusa da na ƙarshe da suka buga a Casablanca na Morocco.
Myriam Maéva Nyadjou Wamen ce ta jefa ƙwallon da ta bai wa Kamaru nasara a minti na 19 na wasan.
Super Falcons ta matsa lamba sosai musamman a ƙarshen rabin farko da kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, amma ta kasa samun ƙwallon rama.
Mai tsaron ragar Kamaru ma ta yi wata muhimmiyar ceto a rabin na biyu, inda ta hana Najeriya samun ƙwallon da za ta yi kunnen doki.
Wannan rashin nasara ya kawo ƙarshen burin Super Falcons na kare kambunta, tare da hana ta samun gurbin zuwa wasan kusa da na ƙarshe.
Haka kuma, sakamakon ya sa Najeriya ba za ta samu tikitin kai tsaye zuwa gasar cin kofin duniya ta mata ta 2027 da za a gudanar a Brazil ba, wanda ake bai wa ƙasashen da suka kai wasan kusa da na ƙarshe na WAFCON.
Kamaru za ta kara da Morocco a wasan kusa da na ƙarshe, bayan Morocco ta doke Afirka ta Kudu da ci biyu da ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login