Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kano: Dattijuwa mai shekara 73 ta yi saukar alƙur’ani

Published

on

Hajiya Binta Muhammad Bakanbare na cikin ɗaliban da suka yi sauka a makarantar gidan Malam Abdussalam da ke Yakasai a ƙarshen makon da ya gabata.

Hajiya Binta mai shekara 73 a duniya ta shaida wa Freedom Radio cewa, daman tana da shauƙin karatun alƙur’ani mai girma tun tana yarinya.

Sai dai an yi mata aure tana shekara 13, to amma shekara 8 da suka gabata sai ta riƙa bibiyar makarantu inda ta sake bita sannan ta ɗora a inda ta tsaya.

Sayyada Saudatuz-Zam’an Sheikh Nasir Kabara ita ce, malamar da Binta ta yi sauka a hannunta, ta ce, Bintan ɗaliba ce zaƙaƙura wadda ke kere sa’a a cikin ɗalibai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!