Connect with us

Coronavirus

Karin mutum 2 sun rasu sakamakon Covid-19 a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce an samu karin mutum 2 da suka rasu, daga cikin wadanda suka kamu da cutar Covid-19 a jihar.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ce ta bayyana hakan cikin wata samarwa da ta fitar a shafinta na Twitter a daren Larabar nan.

Sanawar ta ce a ranar Laraba kadai an samu karin mutane 24 da suka kamu da cutar Covid-19 a jihar Kano.

A yanzu haka dai jimillar wadanda suka kamu da cutar a Kano sun kai mutane 139.

Sannan mutane 5 daga ciki sun rasa ransu sanadiyyar cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!