Labarai
An dage cigaba da shari’ar zargin wacce ta tsallake rijiya da baya a Sauddiya
Babbar kutun tarraya dake da zama a gyadi-gyadi dake nan Kano karkashin jagoranci me shari’a lewis Allgoa ta dage sauraran shari’ar da ake zargin wasu mutune shida bisa sanyawa wata yarinya me suna Zainab Habibu Aliyu kwaya a cikin Jakarta a yayin da zata tafi kasa mai tsarki tare da iyayen ta.
An dai sanya ranakun 21 zuwa 22 ga watan Nuwanban domin cigaba da shari’a, kan wannan zargin da ake yi wa wasu ma’aikatan filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Mutune shidan da’ake zargi sun hada da Idiris Umar wanda aka fi sani da Umar sanda da Sani Suleman da Nuhu Adamu da kuma Rhoda Adetungi Udosen Itoro Henry, Sai kuma Sani Hamisu .
PDP ta yi korafi kan mai Shari’a Zainab Bulkachuwa
Kotu ta cigaba da sauraron shari’ar Malam Shekarau
An dage yanke hukunci a shari’ar takardun makarantar Shugaba Buhari
Haka kuma a jiya ne Lauyan hukumar hana sha da fataucin kwayoyi Barista Femi Oloruotumba ya gabatar da shedu biyu daya hada da wace tashirya tafiyar Hajiya Rabi Umar wacce mahaifiya ce ga Zainab Aliyu tace tabaiwa me Auna kaya jakukkuna uku, yayin da suke shirye-shiryen zuwa kas amai tsarki
A cewar ta, ta baiwa mai suna Salisu Alasan Bako shi kuma yake tabbatar wa kotun cewar Hajiya Rabi Umar tabashi jakukkuna uku da Fasfonan tafiye-tafiye uku kuma nan take ya aike da su zuwa daki matafiya, don tantancewa wanda bisa al’ada ake yi wa fasinjoji.