Kiwon Lafiya
KWALARA: Sama da mutane dubu 30 ne suka kamu da cutar a Najeriya – NCDC
Cibiyar dakile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta ce, adadin waɗanda suka kamu da cutar kwalara a ƙasar nan ya kai dubu talatin da uku da ɗari shida da sittin daya a jihohi ashirin da uku.
Haka kuma wasu dari tara da talatin da uku sun rasa rayukan su saboda cutar ta kwalara.
Ministan muhalli Muhammad Mahmud Abubakar ne ya tabbatar da wannan adadi, yayin da yake yiwa manema labarai ƙarin bayani jiya a Abuja.
Ya ce, akwai buƙatar gaggauta sanar da ‘yan Najeriya yadda cutar ke sake bazuwa da kuma irin matakan da ya kamata su ɗauka don kare kan su.
Gwamnatin Kaduna ta bullo da binciken gida-gida don kare al’umma daga kamuwa da cutuka masu yaduwa
Ya ƙara da cewa a yanzu jihohi 22 ne cutar tayi ƙamari, ciki har da birnin tarayya Abuja, da Benue, Delta, Zamfara, Gombe, Bayelsa, Kogi, Sokoto, Bauchi, da Kano.
Sauran su ne, Kaduna, Plateau, Kebbi, Cross River, Neja, Nasarawa, Jigawa, Yobe, Kwara, Enugu, Borno, Kastina, sai Adamawa.
You must be logged in to post a comment Login