Manyan Labarai
Majalisar wakilai ta sake magantuwa kan wutar lantarki
Majalisar wakilai ta koka game da rashin wutar lantarki a fadin kasar nan wanda ta ce lokaci ya yi da ya kamata a lalubo bakin zaren matsalar, da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa.
Shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan a wani zama da majalisar ta yi, don bincika tare da yin nazari kan matsalar wutar lantarkin.
A cewar sa, gwamnatocin baya sun ware makudan kudade don kawo karshen matsalar amma abun ya ci tura.
Majalisar wakilai ta nemi INEC ta dawo da rarar kudin zaben 2015
Hukumar NERC zata soke lasisin kamfanonin raba wutar lantarki
Mambobin Jam’iyar PDP a majalisar wakilai sun musanta rade-rade da akeyi
Shugaban majalisar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa a yayin tattaunawar Ahmed Wase ya ce, idan har ana son tattalin arzikin kasar nan ya bunkasa kamata ya yi a samar da wutar lantarki mai dorewa da nufin farfado da kananan masana’antu da kamfanoni da dai sauran su.
You must be logged in to post a comment Login