Labarai
Masu garkuwa sun kashe dan majalisa a Bauchi

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun hallaka dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Baraza da Dass dake jihar Bauchi Alhaji Musa Mante a ranar Alhamis.
Rahotani sun bayyana cewa bayan hallaka Dan majalisar ‘yan bindigar sun kuma yi garkuwa da matansa guda biyu da kuma Dan sa daya, a gidansa dake karamar hukumar ta Dass.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauschi DSP Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin.
DSP Ahmad Wakil y ace, tuni suka baza jami’an su domin gano wadannan suka aikata.
You must be logged in to post a comment Login