Labarai
Matasa sun yi zanga-zanga kan aikin Titin Five Kilometer
Wasu dandazon matasa maza da mata ne suka fito dauke da kwalaye da rubuce-rubuce a karamar hukumar Rimingado inda suke nuna bacin ransu dangane da yanayin da titin da aka fara yin aikin sa na “five- Kilometer” Yake ciki na lalacewa
Matasan sun bayyana cewa sama da shekara biyar kenan da barje musu titin wanda yake kan titin Gwarzo da nufin gyara shi amma har kawo yanzu babu wani abu da akai wanda yake nuna alamun za’a gyara musu titin
Da suke fadin irin halin da Al’umma Garin na Rimingado ke ciki matasan sun bayyana cewa sakamakon Kurar da take tashi koda yaushe ya haddasawa wasu daga cikin mutanen kamuwa da ciwon numfashi baya ga gurbacewar Ruwan da suke sha.
Haka shima wani da yake gudanar da sana’arsa a gefen titin ya bayyana cewa rashin gyara musu titin ba karamar asara ya janyu musu kuma kan iya zama barazana ga tattalin arzikin su sakamakon kurar da take tashi da ba dare babu rana.
Kungiyoyi sun yi zanga-zanga a Kano
An yi zangazangar kin amincewa da kara masarautu a Kano
‘Yan gudun hijira sun gudanar da zanga-zanga sakamakon yunwa da ta addabe su
Wakilin mu Umar Lawan Tofa ya rawaito mana cewa matasan sun zaga cikin garin Rimingado inda daga bisani suka fito zuwa babban titin da suke magana akai tare da jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a garin