Labarai
Za’a mayar da NNPC hannun ‘yan kasuwa- Mele Kyari
Gwamnatin tarayya ta ce za ta mika ragamar gudanar da harkokin matatun man kasar nan ga bangarori masu zaman kansu da zarar an kammala gyaran da ake yi musu.
Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC Malam Mele Kyari ne ya bayyana haka yayin zantawa da wani gidan talabijin.
Ya ce idan an kammala garambawul da ake yi ga matatun man kamfanin NNPC zai shiga yarjejeniya da bangarorin masu zaman kansu wadanda za su karbe ragamar kula da matatun man.
LABARAI MASU ALAKA
Kamfanin NNPC ya tallafawa asibitin Aminu Kano
NNPC zai fara aikin yashe tafkin Chadi da ya Santana ruwa yankin Gongola
NNPC:ya sanya hannu kan takardar fahimtar juna da jami’ar Bayero
Malam Mele Kyari ya kuma ce kamfanin NNPC zai daina kula da matatun man maimamakon haka zai cimma yarjejeniya da bangarorin masu zaman kansu wadanda za su zuba jari sannan su rika kula da harkokinsu na Kyau nda kullum.
A cewar sa daukar wannan mataki ya zama wajibi domin tsawon shekaru gwamnati na kashe makudan kudade wajen kula da matatun man sai dai a wannan lokaci akwai bukatar sake salo domin farfado da matatun su rika biyan bukatun da yasa aka kafa su tun da fari.
You must be logged in to post a comment Login