Labaran Kano
Muhammad Garba ya ja hankalin ‘yan jaridu
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano kwamaret Muhammad Garba ya ja hankalin kungiyoyin ‘yan jaridu na gidajen rediyoyi dasu mayar da hankali wajen gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da adalci.
Kwamishinan yayi wannan kira ne ta bakin shugaban kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen jihar Kano Kwamaret Abbas Ibrahim wanda ya wakilci kwamishinan yayin rantsar da sabbabin kungiyar ‘yan jaridun gidajen rediyo na Kano.
Abbas Ibrahim ya ce ‘yan jarida suna da muhimmanci a rayuwar al’umma domin suna kokari wajen gano matsalolin dake damun al’umma a kowane mataki.
Gwamnatin Kano ta rinka baiwa ‘yan jaridu hadin kai- Ammai Mai Zare
DW na bada horo ga ‘yan jaridu a Abuja
Nassarawa:An sace tare da garkuwa da mai dakin shugaban kungiyar ‘yan jaridu
A nasa jawabin sabon Shugaban kungiyar ‘yan jaridun gidajenn rediyo na Kano, Nura Bala Ajingi ya ce zai yi kokari wajen ganin ya sauke nauyin da aka dora masa.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa ‘yan jaridu da dama ne daga gidajen rediyoyi daban-daban na Kano suka halarci taron.
You must be logged in to post a comment Login