Labarai
Mun baza jami’ai 200 domin cafke masu sayan kuri’a yayin zabe- EFCC
Hukumar yaki da cin hanci da rashwa ta EFCC ta ce, ta tura jami’anta 200 zuwa jihohin Kano da Jigawa da Katsina domin yaki da masu sayen kuri’u yayin zaben gwamna da ‘yan majalisar dokoki da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban hukumar ta EFCC shiyyar Kano Farouk Dogondaji ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai da safiyar yau Alhamis.
Ya ce, sun tura jami’ai hamsin domin sanya ido kan yadda zaben zai gudana a jihar Kano, sai wasu jami’ai hamsin su ma a jihar Jigawa, yayin da aka tura wasu jami’ai hansin jihar Katsina domin hana sayen kuri’u a lokacin zaben.
A cewarsa sauran jami’an an tura su zuwa filin jirgin saman Malam Aminu Kano da kuma filin jirgin saman Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
Farouk Dogondaji ya kuma ce, tura jami’an na daga cikin kudirin hukumar EFCC na tabbatar da sahihin zabe.
You must be logged in to post a comment Login