Siyasa
Mun dakatar da yin zanga-zanga- NNPP

Jam’iyyar NNPP ta ce, ta dakatar da zanga-zangar lumana da ta shirya gudanarwa yau Alhamis a jihar Kano domin nuna kin amincewa a kan soke zaben gwamna da jam’iyyar APC ta yi.
Shugaban jam’iyyar Umar Haruna Doguwa, ne ya bayyana hakan,yana mai cewa za su bayyana abinda za su yi maimakon zanga-zangar.
Haka kuma ya ce, sun dakatar da yin zanga-zangar ne domin neman zaman lafiyar jihar tare da neman albarka a cikin watan Ramadan da muke ciki.
Umar Haruna Doguwa ya ci gaba da cewa za su fada wa magoya bayan jam’iyyar abinda ya kamata su yi maimakon gudanar da zanga-zanga.
You must be logged in to post a comment Login