Labarai
Mun kai mutane 9 kotu bisa zargin su da sayan kuri’a yayin zabe- EFCC
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar Kano, ta ce, ta kama mutane da dama bisa zargin su da aikata laifin sayen ƙuri’u da raba kayan abinci domin a zaɓi jam’iyyun su.
shugaban hukumar shiyyar jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina Faruk Dogon Daji, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawarsa da Freedom Radio.
Haka kuma ya kara da cewa, tuni hukumar ta miƙa mutane tara kotu cikin wadanda ta cafke din a jihohin Kano da jigawa da Katsina.
Faruk Dogon Daji ya kara da cewa hukumar ta EFCC, ta shirya tsaf wajen ganin an gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi lami lafiya.
Kunna Bidiyon kasa domin kallon cikakkiyar tattaunawar.
https://www.youtube.com/watch?v=BNp9vy6biPg
You must be logged in to post a comment Login