Labarai
Mun sa kafar wando daya da masu safarar miyagun kwayoyi a Kano – NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce, yanzu Jihar Kano na matakin na shida a bangaren sha tare da ta’ammali da miyagun kwayoyi idan aka yi la’akari da jihar legas wadda take a mataki na daya.
Babban kwamanda a hukumar reshen jihar Kano, Dakta Ibrahim Abdul ne ya bayyana hakan a yau ta cikin shirin ‘Barka Da Hantsi’ na nan tashar Freedom Radio, wanda ya maida hankali akan matsalar shaye-shaye a fadin kasar nan.
Dakta Ibrahim Abdul ya ce, hukumar ta yi nasarar kama kwayoyi da aka shigo da su daga wasu ‘yankuna da suka hadar da taban Wiwi bakwai da kuma hodar ibilis guda hudu, sai kuma tramadol da sauraran su.
Karin labarai:
Akwai sauran rina a kaba, a yaki da miyagun ‘kwayoyi a Kano – inji ‘Yan Magani
Da mu za’a kawo karshen shaye-shayen miyagun kwayoyi –ALGON
Hukumar ta kuma koka bisa yadda ta ce kotu na bayar da belin wanda aka kama da shigo da miyagun kwayoyin ba tare da an gama binciken ba.
Kwamandan ya kara da cewa, daga cikin babbar matsalar da hukumar ke fuskanta akwai karancin kayayyakin aiki, wanda ke haifar da koma baya ga hukumar wajen gudanar da aikin ta yadda ya kamata.
Dakta Ibrahim Abdul ya kuma ce, akwai horo mai tsanani akan dukkanin ma’aikacin hukumar da aka kama da taimakon masu shigo da kwayoyin cikin jihar nan.
You must be logged in to post a comment Login